Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A ranar Lahadi, 5 ga Afrilu, 2026, mayakan Hizbullah sun kai hari kan wani jirgin ruwan Isra'ila a tazarar mil 68 daga gabar tekun Lebanon, wanda ke shirin kai hare-hare a ƙasar Lebanon.
An gudanar da aikin kai harin ne ga jirgin da aka nufa da makami mai linzami na ruwa bayan sa'o'i da yawa ana sa ido kan jirgin da aka hara, kuma an tabbatar da samun jirgin kai tsaye.
Sannan Hizbullah ta ce: Mun kai hari kan ababen more rayuwa na sojojin Isra'ila a garin Yusud Hamala, da kuma garin Kafrazwald da ke arewacin Falasdinu.
A na su rahoton kafofin yada labaran Isra'ila sun ce: Jirgin da Hizbullah ta kaiwa hari da makami mai linzami na cikin teku a Beirut wani jirgin ruwa ne na sojojin Burtaniya.
Ra'ayinka